--
Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya Bai Wa Gwamnatin Abba Shawarwari

Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya Bai Wa Gwamnatin Abba Shawarwari

>

 Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya Bai Wa Gwamnatin Abba Shawarwari

A wata hira da yayi da Jaridar The Sun, Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya bai wa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf shawarwarin yadda zai tafiyar da gwamnatin sa. 

Alhaji Tanko Yakasai Ya yi tsokaci game da batun siyasa da kuma sabuwar gwamnatin tarayya da ta Kano da aka rantsar a Mayun 2023.  

Kamar yadda ake cewa siyasar Kano sai Kano, tsohon ‘dan siyasar ya ce tun fil azal haka ake yi a jihar Kano, ana canza gwamnati daga jam’iyya zuwa wata. 

A cewarsa, abu na farko ya kamata Abba ya guji abin da zai jawo masa rigima da mai gidansa Dr Rabiu Musa Kwankwaso, kuma ya yi hattara game da tsige Sarakunan Kano.  

Alhaji Tanko Yakasai ya shaidawa jaridar The Sun cewa, sai daga baya zai iya gane gudun ruwan Abba Kabir Yusuf, ya ce a halin yanzu gwamnan bai dade da fara mulki ba. 

"Ina ganin cewa ya kamata mu saurari Gwamna Abba, mu ba shi lokaci mu ga yadda zai shawo kan matsalolin jihar." 

"Mu na da ‘Yan Gandujiyya da ‘Yan Kwankwasiyya, dukkansu ba su yi bayanin yadda za a magance matslolin ba."

"Zan jira in ga inda Abba zai ba fifiko da matsalolin da zai magance, in ga ko ya kama hanyar gyara, sai in auna shi." 

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na ruguza gine-gine da ta ce an yi su ba a kan ka’ida ba, dattijon yana da ra’ayin akwai matsala game da lamarin.  

Yakasai yake cewa idan har za a rusa gidaje da gine-ginen jama’a, ya kamata a bar doka tayi aiki, ba abin da zai iya bada damar yin bita-da-kulli ba. 

Ban san me Kwankwaso yake so a nan gaba ba. Amma ban jin dadin gwamnati ta karbi mulki ta fara tsige mutanen da magabatanta su ka nada ba.  

Domin hakan zai jawo da zarar an canza gwamnati, a cigaba da yin irin haka. Wannan zai kawo a rika kawo tsare-tsare saboda ramuwar gayya a cewar dattijon.

CREDIT.LIVERTY FM 

 https://chat.whatsapp.com/Ib66myTN1AV9AE8Zi0A4Ra

0 Response to "Dattijo Alhaji Tanko Yakasai Ya Bai Wa Gwamnatin Abba Shawarwari"

Post a Comment