--
ALHAMDULILLAHI :ALHAMDULILLAH: An fara saida buhun Masara Naira dubu 20,000.

ALHAMDULILLAHI :ALHAMDULILLAH: An fara saida buhun Masara Naira dubu 20,000.

>

 ALHAMDULILLAH: An fara saida buhun Masara Naira dubu 20,000. 

Wannan itace kasuwar da ake kira da suna Kasuwan Gari, dake karamar hukumar Kayama jihar Kwara, babbar kasuwa ce dake ci a ranakun Alhamis da Asabar. A ranar Alhamis da ta gabata ana saida buhun Masara Naira dubu 33,000, ana saida buhun Dawa Naira dubu 35,000 a kasuwar.

A wayewar garin yau Asabar Sarkin Kayama ya yi zama da shugabannin kasuwar domin a rage farashin kayayyakin domin tausayawa talakawa, tare da saka dokoki a kasuwar yanzu haka ana saida buhun Masara Naira dubu 20,000 itama dawa ta koma Naira dubu 20,000. 

Kuma ko wanene yaje kasuwar hakan suke saida mishi, ana cigaba da cin kasuwar kamar yadda aka saba. Abokina ne ya ziyarci kasuwar don ganewa idonshi kuma ya dauki wa 'yan nan hotunan masu dauke GPS Map na Adireshin din inda kasuwar take.

Wannan tsarin da Sarkin garin yayi da hadin kan wasu daga cikin shugabannin kasuwar abun a yaba musu ne wanda Insha'Allahu talakawan yankin za su ji dadin shi sosai. Insha'Allahu wannan shine silar karyewar kayan masarufi a Najeriya. 

CREDIT:COMR ABBA SANI PANTAMI. 

0 Response to "ALHAMDULILLAHI :ALHAMDULILLAH: An fara saida buhun Masara Naira dubu 20,000. "

Post a Comment