--
Tofa A sabon watan July da zamu shiga Litar Man Fetur za ta koma Naira 700 a Najeriya, Inji 'yan kasuwa.

Tofa A sabon watan July da zamu shiga Litar Man Fetur za ta koma Naira 700 a Najeriya, Inji 'yan kasuwa.

>

 A sabon watan July da zamu shiga Litar Man Fetur za ta koma Naira 700 a Najeriya, Inji 'yan kasuwa.

'Yan kasuwar dake harkar Fetur na hasashen cewa da yiwuwar litar Man Fetur ta kai Naira 700 a Arewacin Najeriya a sabon watan da za'a shiga na July.

Mike Osatuyi jigo a kungiyar dillalai da masu safarar man fetur din ya ce a kudancin Najeriya farashin litar man na iya haura Naira 700 madamar suka fara shigo da man da kansu daga farkon Watan July. 

A yanzu haka gidajen Mai anan Arewa suna siyar da kowace Lita akan farashin 550 ko sama da haka 'yan bunburutu suna siyar da Lita Naira 700 ko sama da haka. 

Matukar 'yan kasuwar mai suka kara farashi ya koma 700 Gidajen mai da dama zasu siyar sama haka 'yan bunburutu kuma sai yakai 900 ko sama da haka. 

Wannan tsadar da 'yan kasuwa suke son su karawa Fetur wallahi zallar mugunta ce ga talakawan Najeriya, dame talaka zaiji da tsadar Fetur? Ko da tsadar kayan masarufi ko da tsadar kudin makaranta?

Allah muna rokonka ka shiga cikin wannan lamarin ka kawo mana karshen wahalar tsadar rayuwar da muke ciki. 

✍️ Comr Abba Sani Pantami

CREDIT. Labari Da Gaskiya via Facebook search. 

0 Response to "Tofa A sabon watan July da zamu shiga Litar Man Fetur za ta koma Naira 700 a Najeriya, Inji 'yan kasuwa."

Post a Comment