--
Amfanin goro a jikin dan adam cikakken bayanin sa

Amfanin goro a jikin dan adam cikakken bayanin sa

>





Menene gudunmawar goro a cikin Dan Adam


Goro yana ba da gudunmawa a cikin dan Adam, amma ko wanna irin aiki yakeyi. Muhammad Dahir, dalibi mai neman ilimin yadda jikin dan Adam ke gudana a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. ya gudanar da maqalarsa a dakin karatu (seminar room) akan gudunmawar goro a cikin bil Adama. A binciken da ya gudanar, dalibin yace,ciki ya kama daga baki,maqogaro, tumbi,karamin hanji da babban hanji. Goro yana kara gudanar da tafiyar hanji a ciki. Sedai yana bawa sashen(parietal cells) dake samar da sinadarin asid ( hydrochloric acid) a ciki damar samar da asid din sosai. wannan asid din yana haddasa cutar gyambon ciki (gastric ulcer). Goro yana dauke da sinadarin kafen (caffeine) fiye da shayin coffee. wannan kafen yana saka cutar hawan jini (hypertension) ta hanyar toshe kafofin jinin harma da jijiyar da take kaiwa zuciya jini(coronary artery). Bincike ya nuna cewa goro yana kawo tangarda wajen gudanar da aikin koda(kidney) da hanta(liver), sannan yana warkar da ciwon kai tare da hana kamuwa daga cutar ciwon sukari (diabetes). Dan gujewa illar goro, yana da kyau a nisanta anfani da shi don gudun matsala. Muhammad Dahir kuma Allah ya kara basira. Don Allah a sadar da sakon don anfanar jama'ah. mun gode.

Karin bayani 

👇


https://guidanceupdate.blogspot.com/2023/05/menene-gudunmawar-goro-cikin-dan-adam.html

CREDIT 👉👉guidance update blog. 

0 Response to "Amfanin goro a jikin dan adam cikakken bayanin sa"

Post a Comment