--
Rawar da nake takawa a fim bata taba tarbiyya nishaɗi ne kawai inji kilishin Laure

Rawar da nake takawa a fim bata taba tarbiyya nishaɗi ne kawai inji kilishin Laure

>
Jarumin Kannywood Ahmad Yusuf da aka fi sani da Kilishin Laure, ya ce fitowa da yake a matsayin Ɗandaudu a Fim baya ɓata tarbiyya domin yana yi ne kawai domin nishadi.


Ya ce, tarbiyyar kowa daga gida ake fara ta, don haka in mutum ba shi da tarbiyya kar ma ya soma zargar yan fim.


Kilishi ya ƙara da cewa shi ba Ɗandaudu bane kuma ko kaɗan wannan sabgar ba ta birgeshi.


Ya ce burinsa shi ne ya samu auren Jaruma Fati Zinariya da aka fi sani da Hajiya Sara Izzar So.

 

Ga cikakkiyar zantawarsa da shirinmu na Daga Kannywood na wannan makon.

Karin bayani 

👇👇

https://youtu.be/ab-jo6MPwvc

CREDIT 👉Nasiru Salisu Zango via Facebook search. 0 Response to "Rawar da nake takawa a fim bata taba tarbiyya nishaɗi ne kawai inji kilishin Laure "

Post a Comment