--
Abinda yasa muka raba gari da tijjani asasi  kanabaro acikin shirin a duniya sunusi dan yaro.

Abinda yasa muka raba gari da tijjani asasi kanabaro acikin shirin a duniya sunusi dan yaro.

>

Daraktan fitaccen wasan kwaikwayon nan mai dogon zango wato A Duniya Sunusi Ɗanyaro Sani, ya bayyana dalilan da ya sa suka raba gari tsakaninsa da furodusan shirin jarumi Tijjani Asase.


A zantawarsa da Freedom Radio Ɗanyaro ya zargi Asase da yiwa shirin zagon ƙasa da cin dunduniya don kawai Daraktan ya nemi a yiwa shirin kyakkyawan tsari mai ɗorewa don magance sulalewar kuɗi.


Daraktan ya yi bayani filla-filla kan yadda ya riƙa bai wa Asase Miliyoyin kuɗi a kan shirin amma daga bisani hakan ya yi sanadiyyar rushewar alaƙarsu ta tsawon shekaru.


Ya ce wasu daga dattijan masana'antar Kannywood irinsu Malam Ado Ahmad Gidan Dabino sun yi ƙoƙarin ganin an samu daidaito amma lamarin bai yiwu ba domin Asasen ya ce ya riga ya hau teburin naƙi.


Amma duk da haka Daraktan ya sha alwashin ci gaba da gabatar da shirin.


Dangane da waɗannan zarge-zarge Freedom Radio ta tuntuɓi jarumi Tijjani Asase amma ya ce ba zai ce komai a kan wannan lamari ba.

Karin bayani 👇👇

https://youtu.be/H-pCUrMRqKE

CREDIT 👉Freedom Radio Nigeria. 


0 Response to "Abinda yasa muka raba gari da tijjani asasi kanabaro acikin shirin a duniya sunusi dan yaro. "

Post a Comment