--
YANZU-YANZU :Mun fitar da sama da mutane miliyan 100 daga ƙangin talauci -- Gwamnatin Tarayya

YANZU-YANZU :Mun fitar da sama da mutane miliyan 100 daga ƙangin talauci -- Gwamnatin Tarayya

>


Mun fitar da sama da mutane miliyan 100 daga ƙangin talauci -- Gwamnatin Tarayya


Gwamnatin Tarayya ta ce ta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci a faɗin ƙasa.


Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da ta ke wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen taimakawa al'umma.


Ta ce gwamnati ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al'umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki.


Ministar, wacce shugabar shirin a jihar, Beatrice Kitchina ta wakilta, dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata.


Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da 'yan makaranta shi ma.


Sakataren shirin ciyar da 'yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma ya yi amfani a jihar Taraba


CREDIT 👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "YANZU-YANZU :Mun fitar da sama da mutane miliyan 100 daga ƙangin talauci -- Gwamnatin Tarayya"

Post a Comment