--
Yanzu yanzu :Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa bayan an yanke musu hukuncin kisa

Yanzu yanzu :Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa bayan an yanke musu hukuncin kisa

>


Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa bayan an yanke musu hukuncin kisa


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya yi wa wasu fursunoni 12 da aka yanke wa hukuncin kisa afuwa.


A cikin wata sanarwa da mai magana da gidan ajiya da gyaran hali na jihar, SC Musbahu Lawan Nassarawa ya fitar, ta ce gwamnan ya yi wa ɗaurarrun afuwa ne duba da irin cunkoso da ake samu na waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa.


Ya ce tun da farko an yi niyyar yi wa fursunonin afuwa tun a bara, amma hakan bai yi wu ba saboda sai da aka ɗauki lokaci aka tantance su.


Ya kuma ce a yanzu an samu sauki na raguwar mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a gidajen yari bayan afuwa da gwamnan ya yi wa wasu daga cikinsu.


Gwamnan ya kuma yafewa wasu fursunoni mata guda huɗu waɗanda suka shafe tsawon shekaru a ɗaure saboda ganin kyakywan hali da suka nuna a lokacin da suke ɗaure.


An yi kira gare su da su zamo mutane masu kirki bayan komawa cikin al'umma da kuma cewa su guji duk abin da zai sake sa su koma gidan gyaran hali.


Sanarwar ta ce wasu fursunonin da aka yi wa afuwa sun shafe shekaru 25 suna jiran aiwatar da hukuncin kisa a kansu.


(BBC Hausa)


CREDIT 👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Yanzu yanzu :Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa bayan an yanke musu hukuncin kisa"

Post a Comment