--
YANZU-YANZU :CBN ya ƙaryata cewa ya baiwa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Legas kuɗi

YANZU-YANZU :CBN ya ƙaryata cewa ya baiwa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Legas kuɗi

>



CBN ya ƙaryata cewa ya baiwa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Legas kuɗi


Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce bai baiwa Gbadebo Rhodes Vivour, dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour a jihar Legas “ko kobo ba", gabanin zaben gwamnan da za a yi a ranar 18 ga Maris, kamar yadda wata jarida ta kasa ta ruwaito.


Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan bankin, ɓangaren yaɗa labarai, Isa Abdulmumin, ya fitar a yau Litinin.


Abdulmumin, ya ce wannan maganar kwata-kwata karya ce, kuma an yi ta ne domin a bata sunan bankin da ma'aikatan sa.


“An jawo hankalin babban bankin Najeriya kan wani labari da aka buga a jaridar Nation a yau Litinin, 13 ga Maris, 2023, na zargin gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele, ya kaddamar da wani sabon shiri ga zababben shugaban kasa. 


“Muna so mu sanar da jama’a cewa wannan labari kwata-kwata karya ne kuma sharri ne domin gwamnan babban bankin na CBN bai sani ba kuma bai taba haduwa ko ma magana da Mista Rhodes-Vivour ba, ko dai fuska da fuska ko kuma ta hanyar wakili.


"Muna so mu sake jaddada cewa gwamnan CBN ba ya shiga siyasa don haka, muna kira ga duk wanda ke da wani bayani da ya saba wa doka da ya tabbatar da cewa gwamnan hujjojin sa  ta hanyar bayar da wasu hujjoji," in ji shi.

Credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "YANZU-YANZU :CBN ya ƙaryata cewa ya baiwa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Legas kuɗi"

Post a Comment