--
INNALILLAHI WAINNAILAIHI RAJI UN : Rasuwar Abdullahi Abacha akwai tashin hankali - Farfesa Gwarzo

INNALILLAHI WAINNAILAIHI RAJI UN : Rasuwar Abdullahi Abacha akwai tashin hankali - Farfesa Gwarzo

>

TA'AZIYYA: Rasuwar Abdullahi Abacha akwai tashin hankali - Farfesa Gwarzo


Mai Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Hajiya Maryam Abacha, matar Marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar danta, Abdullahi Abacha.


Abdullahi Abacha, mai shekaru 36, shi ne na biyun karshe cikin ‘ya’yan Marigayi Sani Abacha, ya kuma rasu cikin kwanciyar hankali a barcinsa a gidan iyayensa da ke Abuja a ranar Asabar, 4 ga Maris, 2023.


Farfesa Gwarzo a cikin sakon ta’aziyyar da ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a jiya Asabar, ya bayyana rasuwar Abdullahi a matsayin mutuwa mai ban tsoro da damuwa.


Farfesa Gwarzo, wanda shi ne kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano, ya bayyana rasuwar Abdullahi Abacha a matsayin lamari mai tada hankali idan aka yi la’akari da yadda ya rasu yana matashi.


“A madadin iyalai, gamayyar Jami’ar MAAUN, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga mahaifiyarmu Hajiya Maryam Abacha da daukacin ‘yan’uwa bisa rasuwar Abdullahi.” Inji Farfesa Gwarzo a sakon ta’aziyyar.


Da yake jajantawa ‘yan’uwa da abokan arziki, Farfesa Gwarzo ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa dukkan kurakuransa, ya kuma saka sanya shi a Aljannar Firdausi.


Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya bai wa Hajiya Maryam Abacha da daukacin ‘yan’uwa ikon jure wannan babban rashi.


Tuni dai aka binne Marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan da aka yi masa sallar jana’iza a babban masallacin kasa da ke Abuja a ranar Asabar.

CREDIT 👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "INNALILLAHI WAINNAILAIHI RAJI UN : Rasuwar Abdullahi Abacha akwai tashin hankali - Farfesa Gwarzo "

Post a Comment