--
DADUMINSA :Farmarkin Da Wasu Matasa Suka Kaiwa Aisha Humaira A Wurin Zabe A Kano Jahilci Ne Da Rashin Wayewa

DADUMINSA :Farmarkin Da Wasu Matasa Suka Kaiwa Aisha Humaira A Wurin Zabe A Kano Jahilci Ne Da Rashin Wayewa

>


Farmarkin Da Wasu Matasa Suka Kaiwa Aisha Humaira A Wurin Zabe A Kano Jahilci Ne Da Rashin Wayewa


Daga Muhsin Ibrahim


Kamar yadda da yawa kuka sani, ina nazari a kan Kannywood tsawon lokaci. Amma ban san cewar wannan jarumar ba ƴar Kano ba ce sai kwanan nan. Ta yi "trending" saboda ta ce a zaɓi Nasir Gawuna a Kano.


Jiya kuma wasu fisatattun samari sun kusa dukan ta a wajen zaɓe. Ta sha zagi, ƙage, cin mutunci da gorin wai ita da Rarara, wato mai gidanta (Boss), baƙi ne a Kano.


Gaskiya na yi takaici da kuma Allah wadai na wannan abin. Wallahi jahilci ne da rashin wayewa. Ba wani gari ko ƙasa da suka ci gaba ba tare da baƙi ba (watakila ban da Japan da Koriya ta Kudu).


Muna da alheri da yawa a Kano - Alhamdulillahi. Amma mun kasa yaƙar wannan ta'adar ta nuna ɓangaranci. Ni ma na sha gori cewar wai ni Ebira. Duk da ba laifi idan ni shi ne, amma ba ni da alaƙa ta kusa ko ta nesa da Ebira. Iyayena Katsinawa ne. 


Har manyan malamai irin su marigaya Sheikh Ja'afar Mahmud Adam da Dr Ahmad Bamba (BUK) an yi wa gorin gari! Amma duk wanda yake da wayewa, musamman wanda ya zauna a wani gari ko wata ƙasa (iri na), zai yi takaicin wannan halin.


Don Allah mu tashi tsaye wajen yaƙar wannan ƙauyancin. Kai ma zama zai iya kai ka wani garin. Ka yi tunanin yadda za ka ji idan an maka gori. Baaƙi, sau tari, alheri ne. Ku tambayi mutanen Amurka, Ingila, Jamus, dss. idan ba ku sani ba.


Allah ya sa mu gane, mu kuma gyara, amin.


CREDIT 👉Rariya 

0 Response to "DADUMINSA :Farmarkin Da Wasu Matasa Suka Kaiwa Aisha Humaira A Wurin Zabe A Kano Jahilci Ne Da Rashin Wayewa"

Post a Comment