--
Za a ci gaba da zaɓe a jihar Taraba ranar Lahadi

Za a ci gaba da zaɓe a jihar Taraba ranar Lahadi

>Za a ci gaba da zaɓe a jihar Taraba ranar Lahadi


Hukumar zaɓe a jihar Taraba  ta tabbatar da cewa za a ci gaba da zaɓe a jihar har zuwa yau Lahadi.


INEC ta tabbatar wa BBC cewa jihar Taraba na cikin jihohin da za a ci gaba da zaɓen har zuwa Lahadi.


Hakan dai baya rasa nasaba da rashin isar kayan zaɓe a kan lokaci wasu rumfunan zaɓen, kuma intanet ɗin na'urar BVAS na dauke wa.


Haka kuma rahotonni sun ce an yi garkuwa da wasu ma'aikatan zaɓen na wucin-gadi guda uku a ƙaramar hukumar Donga.


Wani jami'in hukumar da ya buƙaci a sakaya sunansa ne ya bayyana wa BBC faruwar lamarin.


To sai dai jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ya ce suna kan gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru.

CREDIT /RARIYA NEWS VIA FACEBOOK SEARCH. 


0 Response to "Za a ci gaba da zaɓe a jihar Taraba ranar Lahadi"

Post a Comment