--
Tofa :Buhari ya gana da Emefiele, gwamnoni da EFCC kan rikicin kuɗaɗe

Tofa :Buhari ya gana da Emefiele, gwamnoni da EFCC kan rikicin kuɗaɗe

>
Buhari ya gana da Emefiele, gwamnoni da EFCC kan rikicin kuɗaɗe


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya gana da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emeifele; shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, da gwamnonin jihohi.


Gwamnonin sun samu wakilcin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da shugaban kungiyar gwamnonin APC, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.


Sauran a taron sun hada da sakataren gwamnatin tarayya SGF, Boss Mustapha, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.


Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa taron ba ya wuce nasaba da karancin kudaden da ake fama da shi na Naira a fadin kasar nan.


Idan dai za a iya tunawa shugaban kasar ya nemi alfarmar kwana bakwai domin samun damar magance wahalhalun da ƴan ƙasa ke fuskanta biyo bayan karancin kudaden da ake samu na sabon kudin Naira.


Babban bankin ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin wa’adin tsohon kudin Naira zai daina amfani a kasar.


Sai dai ‘yan Najeriya da dama na ta kiraye-kirayen a tsawaita wa’adin saboda rashin samun takardun da aka sake wa fasalin.

Source, Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Tofa :Buhari ya gana da Emefiele, gwamnoni da EFCC kan rikicin kuɗaɗe"

Post a Comment