--
Matar da ta aure saurayin ƴarta ba ta yi laifi ba - Hisbah

Matar da ta aure saurayin ƴarta ba ta yi laifi ba - Hisbah

>

 Matar da ta aure saurayin ƴarta ba ta yi laifi ba - Hisbah


Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kammala bincikenta a kan wata uwa mai suna Malama Khadija Rano, bayan an zarge ta da kashe aurenta sannan ta aure saurayin ƴarta.


A sanarwar da kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya fitar a jihar ta ce, bisa rahoton da shugaban kwamitin da aka kafa don binciken lamarin, Malam Hussain Ahmed, ya ce auren ya hallata kuma an yi shi bisa ƙa’ida.


Ahmed ya ci gaba da cewa, “Khadija mijinta na baya, ya sake ta kuma ta kammala idda kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar, inda hakan ya sa ta aure saurayin da ‘yar cikinta ta ƙi yarda ta aura.


Shugaban ya kuma yi watsi da zargin da ake yi wa matar na cewa daga ganin sabon mijin nata ne, ta tilasa wa tsohon mijin ta sai ya sake ta.


Tun da fari matar ta aure saurayin ‘yar cikinta, inda ta ce ba za ta bari su yi asarar mutum mai nagarta irin tasa ba.

Source, Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Matar da ta aure saurayin ƴarta ba ta yi laifi ba - Hisbah"

Post a Comment