--
Ku bani kwanaki 7 zan warware matsalar kuɗi da aka shiga a Nijeriya - Buhari

Ku bani kwanaki 7 zan warware matsalar kuɗi da aka shiga a Nijeriya - Buhari

>

 




Ku bani kwanaki 7 zan warware matsalar kuɗi da aka shiga a Nijeriya - Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ƴan kasar da su ba shi kwanaki bakwai domin ya warware matsalar kudi da ake fama da ita a fadin kasar nan, biyo bayan tsarin da babban bankin Najeriya ya yi na canza manyan kudade na Naira zuwa sababbi.


Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar a cikin wata sanarwa, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a yau Juma’a a fadar shugaban kasa.


Gwamnonin jam’iyyar APC sun je fadar shugaban kasa a Villa ne domin neman mafita kan matsalar tabarbarewar kudade, wanda su ka ce hakan na barazana ga nasarorin da gwamnatin ke samu wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.


A cewar shugaba Buhari, sake fasalin kudin zai kara habaka tattalin arzikin kasar tare da samar da fa'ida ta dogon lokaci.


Sai dai ya nuna shakku game da jajircewar bankuna musamman na samun nasarar manufofin.


"Wasu bankunan ba su da inganci kuma suna damuwa da kansu ne kawai.


“Ko da an kara shekara guda, matsalolin da ke da ala kika da son kai da handama ba za su kau ba,” in ji shi.


Buhari ya kuma ce ya ga rahotanni a telebijin kan yadda ƴan ƙasa ke shan wahala a kan mastsalar canjin kuɗi, inda ya ƙara da cewa a sauran kwanaki bakwai na kwana goma da aka kara kan dena karɓar tsohon kuɗi wajen shawo kan lamarin.


Source, Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Ku bani kwanaki 7 zan warware matsalar kuɗi da aka shiga a Nijeriya - Buhari"

Post a Comment