--
Jarirai 1,000 ake haifa kullum a Kano, in ji tsohon shugaban NCDC

Jarirai 1,000 ake haifa kullum a Kano, in ji tsohon shugaban NCDC

>

 





Jarirai 1,000 ake haifa kullum a Kano, in ji tsohon shugaban NCDC


Tsohon Daraktan Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), Farfesa Abdulsalam Nasidi, ya bayyana cewa a kulli-yaumin ana haifar jarirai dubu ɗaya

a jihar Kano.


Nasidi ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a gidan gwamnatin Kano, yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da kafa kwalejin kimiyyar lafiya ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUST), Wudil, da gwamnatin Kano ke shirin yi.


Kano Focus ta rawaito cewa Farfesan, wanda ya bayyana rahoton mai girgiza mutum, ya nuna damuwa kan raguwar adadin ma'aikatan kiwon lafiya, duk da karuwar yawan jama'a.


Nasidi ya ce: “Ina so in jawo hankalin ku a kan gaskiyar lamari. A yau ma’aikatan jinya na yau da kullum a asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano su 9,900 ne, daya daga cikin asibitocin da suka fi cinkoso a duniya.


“Haka kuma, adadin haihuwa a kullum a asibitn na Murtala ya kai 70 da 350 a kullum a asibitocin jihar. Yanzu idan muka yi la’akari da haihuwa a gida, wanda shi ne mafi yawa, wannan yana nufin muna samun haihuwa kusan 1,000 a Kano kullum.”


A cewar Farfesan, wanda shi ne mai ba da shawara na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, kan cutar AIDS da zubar jini, Najeriya na fuskantar girman al'umma da ya kai fiye da miliyan 218, wanda aka yi hasashen zai karu zuwa miliyan 377 nan da shekara ta 2050, kuma hakan ya faru a lokacin da kasar ta ke fama da likita daya ya duba majinyata 6,000. 

Adadin, in ji shi, ya yi kasa sosai ga shawarar WHO na likita daya ga marasa lafiya 600.


Credit👉 Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 



0 Response to "Jarirai 1,000 ake haifa kullum a Kano, in ji tsohon shugaban NCDC"

Post a Comment