--
Daraktar kamfen din Tinubu, Najatu Mohammed ta fice da ga APC

Daraktar kamfen din Tinubu, Najatu Mohammed ta fice da ga APC

>Daraktar kamfen din Tinubu, Najatu Mohammed ta fice da ga APC


Daraktar kungiyoyin farar hula na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC, Najatu Mohammed, ta fice da ga jam’iyyar mai mulki, inda ta yi murabus daga mukamin darakta na majalisar.


A wata wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Junairu, 2023 kuma zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, Najatu Mohammed ta ce abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa da dimokuradiyyar kasar nan ya sa ba za ta iya ci gaba da shiga harkokin siyasar kasar ba.


Naja Mohammed, wacce ita ce kwamishiniyar kasa a hukumar ‘yan sanda, PSC, ta ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta na bukatar ta ci gaba da fafutukar ganin an samar da kasa mai inganci.


“Wasikar focewa daga jam’iyyar APC kamar yadda sashe na 9.5 (i) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya samar, na rubuto muku ne domin in sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar APC,” kamar yadda wasikar ta bayyana.


“Ina da wannan wasiƙar kuma na sanar da ku murabus di na a matsayin Darakta na Hukumar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na APC. Babban abin alfahari ne yin aiki tare da ku don ba da gudummawa don gina al'ummar mu mai daraja.


“Duk da haka, da dama daga cikin abubuwan da su ka faru a baya-bayan nan a fagen siyasa da dimokuradiyyar kasar, sun sa ba zan iya ci gaba da shiga harkokin siyasar jam’iyya ba. Kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yau na bukatar in ci gaba da fafutukar ganin an samar da ingantacciyar kasa da lamiri mai kyau yayin da na ke ci gaba da kasancewa da cikakken biyayya ga kasata Najeriya.


“ina mai miƙa godiyata ga shugabancinka a matsayinka na Shugaban Jam’iyyar APC. Allah albarkaci tarayyar Najeriya.”


SOURCE /CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Daraktar kamfen din Tinubu, Najatu Mohammed ta fice da ga APC"

Post a Comment