--
ALHAMDULILLAH: 'Yar Talla Mai Sallah Ta Samu Gudummawar Sama Da Dubu 800 Daga Wajen Al'umma

ALHAMDULILLAH: 'Yar Talla Mai Sallah Ta Samu Gudummawar Sama Da Dubu 800 Daga Wajen Al'umma

>

ALHAMDULILLAH: 'Yar Talla Mai Sallah Ta Samu Gudummawar Sama Da Dubu 800 Daga Wajen Al'umma

Jimillar gudunmowa da aka hadawa Hauwa'u ya kama naira dubu dari takwas da goma sha daya da naira dari biyu da tamanin, 811,280.

A yau din nan za mu fara yi mata siyayya kuma Insha Allahu zuwa gobe ko jibi zan yi muku bayanin abubuwan da muka saya da kudin dalla-dalla da kuma abinda za a yi da sauran kudin.

Kuma har yanzu kofa a bude take muna jiran shawarwari daga gare ku akan me da me ya kamata a yi da wannan kudi.

Ga wadanda suka bada gudummawa ta kudi da wadanda suka yi mana addu'a da fatan alkhairi da wadanda suka bayar Da shawarwari Allah ya sakawa kowa da alkairi, Allah ya biya mana bukatunmu na alkairi gaba daya.

Daga Abdulmutallib Hamza Kibiya

Source /Rariya via Facebook search. 

0 Response to "ALHAMDULILLAH: 'Yar Talla Mai Sallah Ta Samu Gudummawar Sama Da Dubu 800 Daga Wajen Al'umma"

Post a Comment