--
Nan Ne ƙofan Garin Samudawa Mutanen Annabi Saleh (AS).

Nan Ne ƙofan Garin Samudawa Mutanen Annabi Saleh (AS).

>

 













Nan Ne ƙofan Garin Samudawa Mutanen Annabi Saleh (AS).


Ana Kiran Wajen Da Suna (Mada’in Salih) Ko Al-Hijr Da Larabci, (ٱلْحِجْر‎‎), Yankin Ya Na Al-‘Ula A Cikin Lardin Madina A Hejaz, Saudi Arabiya.


A Shekara Ta Dubu Biyu Da Takwas (2008), Hukumar Kula Da Adana Kayan Tarihi Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) Ta Ayyana Mada’in Salih A Matsayin Wani Wajen Da Take Girmamawa, Wurin Tarihi Na Hegra Ya Na Kilomita 20 (12 mil) Arewa Da Garin Al-‘Ula, 400 km (250 mi) Arewa Maso Yammacin Madina, Da Kilomita 500 (310 mi) Kudu Maso Gabas Na Petra.


Jordan Bisa Ga Faɗar Alƙur’ani Mai Tsarki Da Hadisai, Samudawa sun wanzu Shekaru Ɗari Bakwai Da Goma Sha Biyar (715) Kafin Haihuwar Annabi Isa (AS) A binciken Kayan Tarihi A Wannan Lokacin A Cikin Kogon Dutse Da Kan Duwatsun Yashi Da Rubutattun Bayanai, Wadda Masana Suka Ɗauka Rubutun Lihyanite Ne Wata Ƙabilar Larabawa.


A Saman Dutsen Athleb, Kusa Da Hegra (Mada’in Salih), An Rubuta Su Zuwa Ƙarni Na Uku Zuwa Biyu Kafin Haihuwar Annabi Isa AS.


Mutane Daga Sassa Daban-Daban Daga Duniya Kan Ziyarci Wurin, Domin Ganin Ƙudiran Ubangiji.


Daga Shafin Taskar Nasaba


SOURCE /CREDIT /ALFIJIR HAUSA VIA FACEBOOK SEARCH. 

0 Response to "Nan Ne ƙofan Garin Samudawa Mutanen Annabi Saleh (AS)."

Post a Comment