--
ME YASA AKE BOYE KARUWANCIN MAZA A BAYYANA NA MATA

ME YASA AKE BOYE KARUWANCIN MAZA A BAYYANA NA MATA

>

 ME YASA AKE BOYE KARUWANCIN MAZA A BAYYANA NA MATA 


Duk binciken da na yi ko na karanta an yi, ya nuna cewa saboda kudi mace take karuwanci ba don son iskanci ba. Iskanci a karshe yake zuwa a sana’ar karuwanci amma neman kudi shi ne kan gaba. 


To amma kwastomomin karuwai, wato maza, iskanci ne yake kaisu. Kudinsu suke warewa su zuba domin su ji dadi ba wata bukata ce da su ta daban ba. Kenan dai maza ne cikakkun yan iskan ba mata ba. Su suke zuba kudinsu a haram ita kuma ta karba ta hanyar haram. 


Amma don rashin mutunci sai ka ga ba a tsani namiji mai yawon ta-zubar kamar yadda aka tsani mace mai tafiya neman kudi ba. Namiji zai gama yawon iskancinsa ya dawo a bashi aure amma mace ko mai nadamarta sai an zageta an mata gori.


Source/credit /Aiha K Nass via Facebook page. 0 Response to "ME YASA AKE BOYE KARUWANCIN MAZA A BAYYANA NA MATA "

Post a Comment