--
Malam Idan kana son AURE, ka nemi KUƊI,  Idan kana neman KUƊI, ka riƙe SANA’A.

Malam Idan kana son AURE, ka nemi KUƊI, Idan kana neman KUƊI, ka riƙe SANA’A.

>

 IMAGE SOURCE /CREDIT /FACEBOOK SEARCH. 


Idan kana son AURE, ka nemi KUƊI,

Idan kana neman KUƊI, ka riƙe SANA’A.


Mu gaya wa kanmu gaskiya, BAN CE AURE BA YA TSADA BA, AKWAI TAKURA, amma da yawancinmu, mu matasa, masu maganar a soke lefe, ba ‘lefe’ kaɗai ke hana aure ba, rashin abin siyan lefen ne (kuɗi), shi kuma kuɗi ba ya samuwa sai da sana’a (sai dai idan ‘kyauta’ ko ‘gado’ za ka samu). 


Matuƙar kana da kwakkwarar sana’a, lefe bai kai ‘mallakar muhalli’ ba wahala (musamman a irin yankinmu, Hadejia; dole sai ka mallaki muhalli tukun a ba ka aure, ko ka fara maganar aure), kuma ‘lefe’ bai kai ɗawainiyyar zaman aure ba (shi za ka iya yi a hankali, a amma a gidan aure, wani abu zai iya taso ma, na kuɗi, bagatatan).


A fahimtata, idan namiji ma ya sayi kayan lefen, KANSA YA YI WA, domin kayan ‘sawa’ ne, da na ‘kwalliya’, kuma da su matar za ta na yi wa ango ‘kwalliya’, har ya kalla ya ji daɗi da nutsuwa. Hasali, yin kayan lefe gwaji ne ga namiji don ya nuna kwazo da jajircewa da nuna cewa, da gaske yake. Matsalar shi ne, idan aka tsaurara, ko aka maida shi tamkar wajibi (idan babu shi, ba aure).


Kuma su ma ai ‘iyayen mace’ suna da ta su hidimar, suna siyan kayan ɗaki (furniture), kayan kitchen, ga garar abinci (wanda a ƙalla sai ka yi wata guda, ko fiye ba ka nemi abinci ba). Waɗannan kayan, idan ka lissafa, a ƙalla sun kai, ko ma su fi kuɗin da miji zai kashe don yi lefe. Duk dai taimakekkeniyya ne. 


Idan kana son aure (musamman a yau), ka yi ƙoƙarin tsayawa da ƙafafunka, ka kasance kana da wata harka ta samun kuɗi; domin bayan hidimar aure, akwai zaman aure, wanda kullum nauyi ne ke ƙaruwa.


Wani abin lura ma kuma, idan neman kuɗinka iya na neman aure ne, ba tare da kwakkwarar sana’a ba, shi ne idan mutum ya yi aure, duk zai shiga matsi, ya ƙare, ya jeme, ya fice a hayyacinsa, domin bai 'financial increment' a kuɗin shiga ba.


Sana’a (aiki, kasuwanci, aikatau…) ita ce ƙofar samun aure, hidimar aure, da kuma dawwama a gidan aure. Allah Ya wadata mu daga falalarsa, ya sauƙaƙa mana hanyar neman arziki na halal.

SOURCE /CREDIT /SIRRIN RIKE MIJI ON FACEBOOK SEARCH. 0 Response to "Malam Idan kana son AURE, ka nemi KUƊI, Idan kana neman KUƊI, ka riƙe SANA’A."

Post a Comment