--
Magana ta gaskiya wannan alamarin yana  matukar cutar da masallata

Magana ta gaskiya wannan alamarin yana matukar cutar da masallata

>
 Barkan Mu da Juma’a 

Yau nayi sallar juma’a a masallacin Malam Aminu Daurawa dake Fagge,domin ni bisa al’ada na kan yi sallah ne a duk inda ta riske ni.

To amma wani abu da ya bani takaici nake ganin kamar ya kamata a duba shine daidai karfe daya da mintuna lokacin da ake sallah a masallacin sai kuma aka kunna karatu a masallacin dake makotaka dashi na sheikh Ahmad Tijjani dake kofar mata, ba wai karatun ne ya bani takaici Ba amma yadda aka kunna shi aka saki lasifika wato amsa kuwwa, daidai lokacin da ake sallah a shi wancan masallacin sai nake ganin kamar bai dace ba,dan kuwa karatun ya sa da yawan wadanda suka bi sahu akan gadar kantin kwari sai da suka yi rafkanwa .

Gashi dai addinin mu guda amma wasu dabi’u da muke nunawa junan mu sai kaga kamar muna sane muke kara rura wutar sabani a tsakanin mu.

Kamata yayi yadda muke da tsananin kishin addinin mu, to mu zama masu tsananin suffanta da addini a mu’amallar mu, babu wanda zai hana jin karatun addini a Kano,amma kuma ya kamata ayi tunani a saka shi lokacin da ya dace, wadannan na yin sallah sai kuyi hakuri a idar domin kaucewa jefa shakku a zukatan masu sallah.

Dan Allah mu ringa hakuri muna cire son zuciya a cikin harkokin addinin mu, Mu kiyaye hakkin abokan zaman mu da makotan mu sai zaman duniyar ya fi yi mana dadi.

Allah ka kara hada kan musulmi amin.SOURCE /CREDIT/Nasiru Salisu Zango via Facebook search. 

0 Response to "Magana ta gaskiya wannan alamarin yana matukar cutar da masallata "

Post a Comment