--
Amfanin aya ga lafiyar dan adam

Amfanin aya ga lafiyar dan adam

>




Image source /credit/Facebook 



 AMFANIN AYA GA LAFIYAR JIKINMU 


Aya tanada matukar amfani sosai kama tun daga ganyenta, saiwarta, da 'ya'yanta.

Ga kadan daga cikin amfanin aya ga lafiyar jikinmu.


1. Aya Na Gina Jiki Cikin Gaggawa.


Sanin sirrin da ke tattare da aya da masana ke da shi sakamakon zuzzurfan bincike da aka gudanar kanta, ya sanya ake amfani da aya wajen gina jiki. Wannan dalili ya sa ake amfani da aya a yankunan dake fama da karancin abinci mai gina jiki. Ana amfani da aya wajen inganta kiwon lafiya ga ma su fama da karancin abinci mai gina jiki sakamakon yawan sanadarai ma su matukar amfani ga jiki da aya ke kunshe da su, kamar sanadaran carbohydrate,magnesium, phosphorus, iron, fiber calcium, sodium, copper, iron da kuma zinc.


2. Maganin Matsalolin Ciki.


Aya na da matukar fa'ida wajen maganin matsaloli da kan shafi ciki. Ba don komai aya ke taka wannan muhimmiyar rawa kan matsalolin ciki ba, sai dai sakamakon wasu sanadarai da ta ke dauke da su, dake inganta wa tare da magance matsalolin ciki musamman wadanda su ka shafi hanji. Sakamakon haka ta ke taimakawa wajen maganin cushewa da kumburin ciki.


3. Gyaran Jiki.


A nan idan ana maganar gyaran jiki mu na nufin inganta lafiyar jiki da suka hada da gyaran fata, gudanuwar jini, kuzarin jiki da sauran su. Yawan sanadaran gina jiki da aya ke da su ya sa ake amfani da ita wajen gyaran jiki, sakamakon haka ta ke gyara fata ta koma kamar ta yaro, ke nan ta zama "Mai da tsohuwa yarinya". Baya ga haka ta na karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzarin jiki.


4. Kara Qibar Jiki.

Aya na taimakawa wajen karawa mutum kiba cikin sauki. Domin samun wannan fa'ida sai a samu aya mai kyau, a daka ta, daga nan sai a zuba ta cikin ruwa ta kwana, idan gari ya waye, sai a tace a zuba sikari a shanye. Haka za a juri yi. Cikin yardar Allah ramar da mutum ke fama da ita za ta gushe ba da jimawa ba.


5. Inganta Rayuwar Aure.

Ba shakka bincike ya nuna yadda aya ke inganta rayuwar aure. Idan mu ka ce rayuwar aure, mai karatu zai gane inda mu ka dosa. Dalili anan shine ta na kara dankon soyayyar ma'aurata ta hanyar taimaka mu su wajen gamsar da junansu a lokacin jima'i. Ba don komai ba sai don amfanin ta wajen kara yawan ruwan maniyyi, sannan ta na karawa mata ni'ima da jin dadi yayin saduwar aure.


6. Kara Ruwan Nono Ga Mata.

Aya na da matukar amfani ga mata ma su shayarwa da ke fuskantar rashin ruwan mama. Saboda haka duk mace mai shayarwa dake fama da wannan matsala ta karancin ruwan nono sai ta dimanci amfani da aya.


SOURCE /CREDIT /sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Amfanin aya ga lafiyar dan adam "

Post a Comment