--
YANZU-YANZU: Mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ta rasu

YANZU-YANZU: Mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ta rasu

>



Image source :daily nigerian Hausa Facebook 



Hajiya Rabi Abdullahi, mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar Kano, Comrade Aminu Abdulsalam ta rasu.


Ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da rasuwar a wani gajeren sako da ya yaɗa ta kafar WhatsApp a yau Asabar.


Sanarwar ta Abba Gida-gida ta ce za ayi jana'izar marigayiyar a masallacin Alfurqan da ke titin Alu Avenue a cikin birnin Kano da misalin ƙarfe 4 na yamma.


Source :daily nigerian Hausa Facebook 

0 Response to "YANZU-YANZU: Mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ta rasu"

Post a Comment