--
Wannan shine babban kalubalen dayake damun duk Da namiji idan ya tashi yin aure

Wannan shine babban kalubalen dayake damun duk Da namiji idan ya tashi yin aure

>


Image source 👉Facebook. 

Hada kayan lefe shine babban kalubalen dayake damun duk Da namiji idan ya tashi yin aure, kuma idan baa kula ba to wallahi wannan alamarin akwai tashin hankali acikinsa.

Zaka ga namiji ya daddage ya takarkare yayi kayan lefe Amma wai kaji mace tace wai kayan ba suyi ba.

Suna Daba hujjar cewa wai ankawowa kawarta kaya dozin dozin saboda haka itama dole sai anmata haka.

Bawai ance kar ai lefe ba amma akwai abubuwan da suke basu dace su zama farilla ba. 

Kuma iyya ye suna bada gudumawa sosai wajan tunzura yara mata akan kayan lefe, 

Wallahi wani kayan lefen idan zaakaishi sai kaga kamar zaa bar kasar mota mota. Bin cike ya nuna, mata dayawa suna son ai musu kayan lefe na kece raini. 

A karshe dai wannan alamarin yana ciwa matasa tuwo akwarya wallahi kuma yana rage niyyar aure, wata illar itace wannan kayan lefen wasu bashi suke ci sukeyi. 

Ya kamata iyyaye su fadakar da Ya'yansu mata akan sukarbi abin da Allah ya horewa samarin su domin a zauna lafiya. 


0 Response to "Wannan shine babban kalubalen dayake damun duk Da namiji idan ya tashi yin aure "

Post a Comment