Tallafin man fetur ba mai ɗore wa ba ne – IPMAN

 


Tallafin man fetur ba mai ɗore wa ba ne – IPMAN


 


Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta ƙasa (lPMAN), ta ce tallafin da ake biya a kan man fetur ba dawamamme ba ne.


Mike Osatuyi, Kwanturolan ayyuka na kasa na lPMAN, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a yau Litinin a Legas, ya yi Allah wadai da biyan tallafin man fetur.


Osatuyi ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karin farashin man fetur a gidajen mai a fadin kasar nan.


Ya ce gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 20.51 a kasafin kudin shekarar 2023 a kan kudaden shiga na Naira tiriliyan 9.7, inda ya bar gibin Naira tiriliyan 10.78.


Osatuyi ya ce gwamnati na fatan bayar da tallafin man fetur har zuwa watan Yunin 2023 kan kudi Naira tiriliyan 3.6, a kan N435 na farashin dala na babban bankin Najeriya (CBN).


“A halin yanzu, farashin a hukumance na CBN ya kai kusan N445 zuwa dala daya wanda ya haura N435 zuwa dala da aka ƙiyasta a kasafin kudin shekarar 2023,” inji shi.


Ya ce tsarin bayar da tallafin ya haifar da ƙaruwar giɓin kasafin kuɗi tare da haifar da koma baya ga rancen tattalin arziki.


Ya kuma ce tallafin ya sa fasa-kwaurin man fetur ya zama sana’a da a ke rububi saboda ribar da ake samu


Source : daily nigerian Hausa on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments