--
SIRRIN ASUBA GA MA'AURATA

SIRRIN ASUBA GA MA'AURATA

>Idan magidanci yana yawan samun sabani da rashin fahimta tsakaninsa da matarsa to lallai su koma raya Sunnah ta Ma'aiki (SAW) bayan Sallan Asuba


Malamai masana halayyar 'dan adam sunyi wani nazari kamar haka, sukace idan dare yayi, ka debo damuwar duniya da gajiya, kwakwalwarka tana caji, ko da ka tara da iyalanki a wannan lokaci ba zaka samu nutsuwa ba


Amma idan kayi bacci, asuba tayi ka tashi kaje Masallaci kayi sallah, kwakwalwarka ta dawo fresh, gajiya da damuwar duniya duka sun tafi, to a wannan lokaci na bayan Sallan Asuba ya dace ka tara da iyali, zaku samu nutsuwa da shakuwa


Saboda a ka'ida kwakwalwa ta fi kama abu bayan gari ya waye, wato ba'a cusa mata damuwar duniya ba, don haka saduwa bayan Sallan Asuba zai sa ka bar gida uwargida na tunaninka, kaima kana tunaninta, saboda shine abinda kwakwalenku suka fara dauka bayan asuba, yana kawar da gaba da kiyayya


Don haka ma'aurata musamman wadanda suke yawan samun sabani da iyalai ku gwada wannan hikima na Malamai


Allah Ya sa a dace

SOURCE :SIRRIN RIKE MIJI ON FACEBOOK. 

0 Response to "SIRRIN ASUBA GA MA'AURATA"

Post a Comment