SHUGABAN FIFA YACE TABBAS SUNYI KUSKURE DA SUKA BA QATAR DAMAR DAUKAR NAUYIN KOFIN DUNIYA

 


Tsohon Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce sun amince cewa sun tafka kuskure wajen bai wa Qatar baƙuncin Gasar Kofin Duniya.


Mista Blatter, mai shekara 86, shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya (Fifa) lokacin da aka bai wa Qatar damar karbar bakuncin gasar a shekarar 2010. 


Kasar Qatar tana shan suka daga Kasashen Yammacin Duniya kan batun auren jinsi da batun kare hakkin dan Adam da zargin muzguna wa ma'aikata baki.


Source :BBCHAUSA Facebook. 

0/Post a Comment/Comments