NIGERIA TAYI FICE A MULKIN BABA BUHARI SABODA KWAREWAR SA INJI YAHAYA BELLO

 
Najeriya Ta Zarce ƙasashe da Yawa a mulkin Buhari domin shugaba Buhari ya yi abinda ya kamata a mulkinsa ~ Inji Yahya Bello.. 


Daga Falalu Lawal Katsina 


Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello na Ya bayyana mulkin Buhari matsayin mulkin daya ɗaga darajar Najeriya ta zarce ƙasashe da dama ta Fannin ci gaba...


Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yace Ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Najeriya ta zarce wasu ƙasashen da ake cewa sun ci gaba. 


Kamar Yadda The Cable ruwaito Gwamnan Yahaya Bello ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Rwang Pam township stadium Jos, babban birnin jihar Filato....


Sai dai gwamnan bai ambaci sunayen ƙasashen da suka riga suka cigaba, waɗanda yake nufin a mulkin Buhari Najeriya ta wuce da ajinsu ba.

SOURCE : KATSINA ONLINE ON FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments