Na daina hawa shafukan zumunta saboda ana yawan zagi na - Tinubu

 

Na daina hawa shafukan zumunta saboda ana yawan zagi na - Tinubu


Ɗan takarar shugabancin Najeriya Asiwaju Bola Tinubu ya ce ya daina hawa shafukan sada zumunta saboda maganganun da ake yi a kan sa na saka masa hawan jini.


Cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumuntar yanzu haka, an ga Tinubu na maganar cewa mutane na yawan zagin sa.


"Na daina karanta [kalaman] shafukan sada zumunta; suna zagi na sosai. Idan na karanta ina samun hawan jini kuma na ji ɓacin rai," in ji shi.


"idan ina son na ji wani abu 'ya'yana ko ma'aikatana za su faɗa min cewa wane ya ce kaza, idan na gaji sai in ce musu ku rabu da su kawai."


A ranar Talata da ta wuce Tinubu ya yi suɓul-da-baka a garin Jos yayin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da kamfe ɗinsa, inda ya kusa kiran sunan jam'iyyar adawa ta PDP a madadin tasu ta APC.


Ya ce: "Allah ya taimaki PD...APC." Hakan ya sa ma'abota shafukan zumuntar suka sako shi a gaba, inda suka dinga barkwanci da tsokanarsa game da tuntuɓen harshen da ya yi.


Bola Tinubu na da jimillar mabiya miliyan biyu da ɗoriya a sahihan shafukan da ke ɗauke da sunansa a dandalin Twitter da Facebook da Instagram.


SOURCE 👉Mikiya Hausa labarai 24 on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments