Ministan kuɗi na Ghana ya nemi afuwa kan matsalar tattalin arziki

 


Ministan kuɗi na Ghana ya nemi afuwa kan matsalar tattalin arziki


Ministan Kudi na Ghana, Ken Ofori Atta a yau Juma'a ya ce ya yi matukar nadama kan matsalolin tattalin arziki da kasar ta tsinci kanta, amma ya kare kansa daga zargin da ƴan majalisar ƙasar ka yi masa na cewa bai cancanci aikin ba.


An soki Ofori-Atta kan yadda ya tafiyar da abin da ya zama matsalar tattalin arzikin Ghana mafi muni a tsawon shekaru.


Hakan ya zo ne a daidai lokacin da ya ke jagorantar tattauna wa da asusun lamuni na duniya, IMF, domin samar da agajin da ya kai dala biliyan uku.


Darajar kuɗin Ghana ma, cedi ta faɗi da fiye da kashi 40 cikin 100 a bana, abin da ya kawo cikas ga masu shigo da kayan masarufi.


A halin da ake ciki, hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya kai mafi girma a shekaru 21 da kaso 40.4 cikin 100 a watan Oktoba sakamakon hauhawar farashin kayayyakin da ake shigo da su.


Dangane da wannan batu, ministan da ke cikin rudani yana fuskantar suka da ‘yan majalisar daga manyan jam’iyyun siyasa biyu na neman a tsige shi daga mukaminsa.


Duk da haka, Ofori-Atta ya kare kansa daga zarge-zargen da aka yi masa a jawabinsa na farko a bainar jama'a kan lamarin.


Source 👇

Daily Nigerian Hausa on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments