Malam ka Farayin Adalci a gidan ka kafin ka zagi Buhari ~ Wike ya Gargaɗi Atiku

 
Malam ka Farayin Adalci a gidan ka kafin ka zagi Buhari ~ Wike ya Gargaɗi Atiku 


Daga Falalu Lawal Katsina 


Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya caccaki dan takarar kujerar shugaban Ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar. Wannan karon, Wike ya ce Atiku munafuki ne kan sukan da ya yiwa shugaban Buhari kan nade-naden da yake yi.


A jawabin da yayi a Jiya Alhamis, 17 ga Nuwamba, Gwamna Wike ya ce babu wani banbanci tsakanin Atiku da Buhari, duk kanwar ja ce.


Wike yace idan Atiku da gaske yake, ya fara tabbatar da adalci cikin jam'iyyar PDP tukun kan ya zargi Buhari. 


Wike bayyana hakan ne yayinda yake kaddamar da titin saman Nkpolu-Oroworokwo dake Port Harcourt, rahoton TheNation. 


Wike ya gayyaci dan takaran shugaban kasa jam'iyya Labour Party LP, Peter Obi, jiharsa don kaddamar da titin sama..


Source 👉👉Fitila Hausa on Facebook. 


0/Post a Comment/Comments