--
MAGANIN CIWON SIKILA FISABILILLAH

MAGANIN CIWON SIKILA FISABILILLAH

>Ciwon Sikila na daya daga ciwukan da yake addaban mutane kuma yake da wuyan magani


Amma ga duk musulmi munyi imani cewa dukkan wata cuta da ubangiji ya saukar bata sauka ba sai da ubangiji ya saukar da maganinta Wanda Allah (s.w.a) ya sanar dashi ya sanar dashi Wanda kuma bai sanar dashi ba to bai sani ba.


Haka shi maganin yakanyi aiki ne da izinin ubangiji shiyasa a kullum nake ganin wauta wajen mai maganin yace nan da kwanaki kaza mutum ya warke tabbas wannan hurumi ne na ubangiji aka shiga, domin idan yaso zai iya sa wani yayi amfani da maganin yasamu waraka wani kuma yayi amfani da maganin yaga bai yi masa ba kwata-kwata.


Abun da akafi so dai shine da mai magani da mai karbar magani ya zamana suna da tawakallin ubangiji ne ke bayar da lafiya sai afi samun nasara wajen maganin.


ALAMOMIN SIKILA


Alamomin cutar sikila bata nunawa daga haihuwa tana fara bayyana ne a tsakanin yara masu watanni biyar zuwa shida.


Wasu daga cikin yaran kan fara samun ciwukan da suka shafi cutar cikin kankanin lokaci wasu daga cikin kuma sai a gaba cutar ke bayyana.


Farkon abubuwan da ake gane cutar sune:


1. Yawan kumburin kafa da hannuwa


2. Yawan kasala


3. Canjawar kalar fatar jiki da idanu zuwa yellow kala wanda a likitance ake kira da jaundice, ko kuma idanun su canza zuwa white kala wanda a likitance ake kira da icteris.


Alamomin wannan cutar suna bambamta daga wannan mutum zuwa wancan, ko kuma ta dalilin canjin yanayi.


Masu ciwon sikila na cikin wadannan hadarurruka wadanda ke jawo ciwo a jiki irin su;


Ciwon baya


Ciwon kirji


Ciwon kafa


Ciwon hannu


Ciwon mara


Wadannan ciwuka na faruwa ne a dalilin gajiya, rashin shan ruwa isasshe, rashin lafiya, canzawar yanayi ko damuwa.


Sannan suna shiga cikin mawuyacin ciwo wanda su kadai suka san irin radadin da suke ji.


Idan kuma SCD din ya yi tsanani yana kawo karancin numfashi, gajiya, juwa, da kuma ciwon gabbai.


Sannan yana damaging din SPLEEN.


Spleen gland ne da ke kasan mara daga gefen hagu, yana tarwatsa tsaffin RED BLOOD CELLS, sannan yana a matsayin rumbu na adana jini.


Yana producing LYMPHOCYTES (a type of WHITE BLOOD CELLS) a jikin d’an Adam.


Rashin karfi ko tarwatsewar SPLEEN yana haifar da abubuwa kamar haka;


A). Blood infection (SEPTICEMIA.


B). Lung infection (PNEUMONIA)


C). Brain & Spinal cord disease (MENINGITIS)


D). Bone Infection (OSTEOMYELITIS)


HANYAR MAGANIN NA FARKO DA AKE MAGANCEWA DA YARDAN ALLAH SHINE;


A samu Sassaken Tsamiya da Kanumfari da Citta sai a dafa shi sosai ya dahu sai a dinga shan karamin Kofi Wanda bai wuce Girman 125 ML ba, sau 3 a rana.


Sai Hanya Ta Biyu Da zaka Magance Matsalar da Yardan Allah.


A nemi Ganyen Taba-taba a kirbasu yana danyen shi tare da farar albasa bayan ankirbasu sai a samu wani waje mai kyau a zuba ciki a zuba ruwa Wanda zai isa daidai sai a rufe tun safe sai yamma a zuba a karamin Kofi asha akuma dibo duddugan ganyen a shafe jiki dashi haka za'ayi har sai ansamu waraka da yardan Allah.


Sai mutum ya zabi hanyar da tafi mashi sauki ya jaraba ta.

Source 👉 Taskar Murtala Kawo on Facebook. 

0 Response to "MAGANIN CIWON SIKILA FISABILILLAH"

Post a Comment