Maganin Ciwon Sanyi Na Gonorrhea Fisabidillah

 Sharadin shine kuyi Sharing domin akwai yan uwa da basu cikin wannan Page ɗin kuma matsalar tana damun su.


Farko menene Gonorrhea?


Gonorrhea dai wani irin ciwon sanyi ne da ke kama jikin dan adam. Gonorrhea akan kira wannan ciwon da "clap" kokuma "drip, a turance. saboda ana daukar wannan ciwo daga wani zuwa wani ko kuma daga Uwa zuwa jaririnta.


Wannan ciwon na Gonorrhea akan dauke shi tabhanyar saduwa da mai wannan ciwon, da zarar Macce ko namiji ya sadu da mai dauke dabwannan ciwon shikenan sai kwayar cuta mai suna Neisseria

gonorrhoeae ta shiga jikin mutum.

Wannan bacteria ta Gonorrhea tana da saurin kama jikin wanda ta shiga domin kuwa bata wuce kwana 2 zuwa 3 ta bayyana.  Ita wannan cutar gonorrhoea a maza takan sa bututun dake dakko fitsari ya kumbura, kuma ya dau ruwa, daga nan sai mutm ya rinka jin zafi wajen fitsari (dysuria), Fitar wani ruwa ruwa me kauri yayin da mutum ya gama fisari (gleet) Haka kuma takan Kumburar da 'ya'yan maraina.


A mata kuma bata cika nuna alamu ba amma wani sa'in bututun dakko fitsarinsu zai kumbura sannan tsokar (cervix) zata kumbura daga nan sai ya haifar mata irin abinda take haifarwa maza. sannan kuma

wannan cutar takan hanawa mata. haihuwa


A nemi wayannan maganukkan, Ofloxacin tab, doxycyline cap, metronidazole 400mg. Sai a sha su na sati 2 in shaa Allahu zai sami Sauƙi da Iznin Allah.


Ko kuma a nemi Hulba a rika dafawa tare da Kwayoyin tafarnuwa ana sha kullum da safe. Sannan a nemi 'Ya'yan cikin BADO, a dakasu sosai. Sannan a samu ganyen RAIHAN shima a dakashi sosai. Sai a samu ganyen Duman Rafi shima a daka shi sosai.


Kowannensu a debi cokali Uku-Uku, Citta da kanumfari ma haka.. A hada da Garin Tafarnuwa cokali Uku, Garin Habbatus sauda shima Cokali uku, Garin Habbur Rashad shima haka. Gaba dayansu sai a juyesu aciki zuma, a gaurayasu a rika shan Cokali uku safe da rana da yamma.


In sha Allahu zaka samu Waraka acikin Qankanin lokaci da yardar Allah. Amma idan namiji ne yake fama da wannan cutar har matarka  zaku dinga sha. Kuma zaku dena Kusantar Juna alokacin da kuke

shan maganin.


Allah yasa adace.


WALLAHU A'ALAM


Source :malama juwairiyya Facebook 

0/Post a Comment/Comments