KWANKWASO, ZAMU KIRKIRI YAN SANDAN JIHOHI DA KUMA GYARA AIKIN POLICE NAKASA

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana shaawarsa na yin garambawul ga 'yan sanda har da kafa ‘yan sandan jihohi a fadin tarayyar kasar nan, muddin hakan ya dace da kundin tsarin mulki.

 

“Idan aka duba tsarin mu, za ka ga cewa a shirye muke sosai don sake fasalin kasa, gami da ‘yan sandan jihohi in ji Kwankwaso a yayin taron The People’s Townhall 2023, wani shiri kai tsaye da gidan talabijin na Channels ya shirya a Abuja a yammacin Lahadi.


"Muna imanin cewa za mu saurari jama’a kuma za mu yi abin da ya dace. A shirye muke mu bi ka’idojin da suka dace muddin ‘yan Najeriya na da sha’awar hakan. 


Amma a daya bangaren, mun yi imanin cewa mafi yawan wadannan abubuwan da ke tafe suna faruwa ne sakamakon gazawar gwamnati. Da zarar komai ya yi kyau, duk waɗannan abubuwa za su gyara kansu.


Source :  rahama tv on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments