Ko yan N-Power batch C suna sane da garabasar WORK NATION da gwamnatin tarayya ta bullo masu da ita kuwa?

 

Ko yan N-Power batch C suna sane da garabasar WORK NATION da gwamnatin tarayya ta bullo masu da ita kuwa?


Gwamnatin tarayya ta kara ɓullo da wani shiri a matsayin garabasa musamman ga yan N-Power batch C1 waɗanda suka cinye wa'adinsu na aikin N-Power a watannin baya kadan da suka gabata.


Hukumar ta N-Power ta saka wata sabuwar manhaja da ma'aikatan N-Power sun bude shafinsu ta adireshin dake kan manhajar NASIM, inda idan suka bude dashboard din nasu daga sama kusa da bangaren da suka yi test za su ga icon na WORK NATION, inda za su bude shi don gudanar da jarabawar gwaji.


Kamar yadda Katsina Daily News sanarwar ya nuna cewa ko ka ci jarabawar gwajin sosai ko ba ka sami maki sosai, sun ce kada a damu, za su yi amfani wajen ba tsaffin yan N-Power batch C1 domin basu horo na musamman, da kuma hada su da damarmaki na ayyukan yi a duk fadin duniya.


Don haka duk waɗanda suka san sun kammala N-Power na rukunin C na farko su gaggawa su gudanar da wannan test din ta WORK NATION.


Daga Muhammad Dagauda


Source 👇

Hasken shiriya on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments