JAHILCI DA RASHIN KULAWA DA KAIDA KE KASHE MASU CIWON SIGA INJI OBASANJO.

 

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya koka da cewa rashin ilimi ko kuma rashin kulawa wajen wayar da kai game da ciwon suga ke janyo mutuwar marasa lafiya da dama.


Obasanjo ya bayyana haka ne a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokutan jihar Ogun, yayin wani wasan sada zumunci tsakanin kungiyar kwallon kafa ta All-Stars Abeokuta da tsohuwar kungiyar Super Eagles.


Gidauniyar Olusegun Obasanjo ce ta shirya wasan a matsayin wani bangare na gudanar da bikin ranar ciwon suga ta duniya ta bana.


Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya ce ya shafe sama da shekaru 40 yana fama da ciwon suga, inda yace cutar ba ta warkewa amma ana iya magance ta.


A cewarsa, mai dauke da ciwon suga na iya rayuwa har zuwa shekaru 100 idan ya bi ka'idodin yi nazarin da likitoci suke gindayawa masu dauke da ciwon na suga.


SOURCE : Rahama Tv on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments