Iyayen yara 70 da maganin tari ya kashe a Gambia sun yi watsi da karɓar diyya
Iyayen yara 70 da suka mutu a Gambia sakamakon shan wani nau'in maganin tari da kamfanin Maiden Pharmaceuticals mallakin India ke yi, sun yi watsi da biyansu dala dubu 20 kan kowanne yaro guda a matsayin diyya daga gwamnatin kasar.


Ma’aikatar mata a Gambia wadda ta sanar da ware tsabar kudin har dala dubu 20 ga kowanne yaro guda don rabawa Iyayen yaran 70 da nufin rage musu radadin rashin 'ya'yan nasu, ma'aikatar ta sake bayyana alhininta kan abin da ta kira ibtila'i.


Sai dai tuni Iyayen yaran suka yi watsi da wannan mataki wanda suka bayyana da cin mutunci a garesu.


Mai magana da yawun Iyayen, Ebrima Sanyang ya ce matukar suka amince da karbar kudin tamkar sun bayar da kai ne game da fafutukar da suke ta ganin an yi musu adalci wajen bin hakkin yaran da maganin tarin ya kashe.


Iyayen yaran sun bukaci hukumar da ke kula da ingancin magunguna ta Kasar ta janye ikirarinta na cewa ambaliyar ruwa ce ta yi sanadiyyar ajalin yaran sabanin gurbataccen maganin da ake ikirari.


Haka zalika, Iyayen sun bukaci dakatar da hukumar kula da Ingancin magungunan ta Gambia daga duk wani bincike da ke da alaka da mutuwar yaran.


A watan Oktoban da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi kan wasu magungunan tari 4, da ta ce ka iya zama sanadiyyar mutuwar gomman yaran a Gambia bayan bincike ya tabbatar da cewa kodarsu ta tabu bayan shan maganin.


Tuni dai India ta dakatar da sarrafa nau'in maganin yayinda ta fara kaddamar da bincike don gano alakarsa da zargin da ake na yiwuwar ya kashe kananan yaran 70 a Gambia.

Source :daily nigerian Hausa Facebook. 

0/Post a Comment/Comments