--
Ina maza? To ga hanyar da zaka zama cikakken na miji nagari a wajan matar ka

Ina maza? To ga hanyar da zaka zama cikakken na miji nagari a wajan matar ka

>

 Image source /credit Facebook. 


TAYAYA ZAN ZAMA MIJI NA GARI?


Zama Miji na gari wani abu ne da ya kamata mu fito da wadansu hanyoyi da za su taimaka mana, wajan zama miji na gari.

Kowa ne dan adam yana da bukatar abokin zama na gari, da zai nuna soyayya, kauna, daukar nauyi da kulawa. Domin samun zamantakewar aure mai aminci da inganci.


Ga yadda zaka gina zamantakewarka da matarka, domin zama miji nagari.


1. Ka zamo mai tattaunawa da abokinyar zamanka, tattauna matsalolinku tare da nemo mafita. Hakan zan kara muku fahimtar juna da tunkarar manufa iri daya ta samun dadin zamantakewar aure.


2. Nemi shawarar matarka akan wasu abubuwan rayuwarku, ko da kuwa baza kai aiki da ita ba. Manzon Allah SAW ya kasance yana neman shawara a wajen matansa, kuma har yai aiki da su.


3. Ku kiyayi karya da rashin gaskiya a cikin iyalanka, domin rashin gaskiya da karya yana kawo raini.


4. Taya matarka ayyukan cikin gida, idan kana gida kenan. Wannan zai kara mata kwarin gwiwar cewa ita kuwa ta samu miji na gari.

5. Wajibi ka kula da damuwarta, matukar kana son kaima ta damu da damuwarka.


6. Ka zamo mai yabo da kalmomi masu dadi ga uwar gidanka. Ka nisanci kyararta ko yi mata fada a gaban mutane.


7. Boye sirrin gidanka da zamantakewarka maras dadi a gidanka.


8. Nuna kauna da soyayya ga matarka, tare da furta gwalagwalan kalmomin raya zuciyar masoya.


9. Sumbatar iyalinka akai akai na kara dankon kauna a junanku.

10. Duk abin da take so, kai ma kaso shi dai dai gwargwadon iyawarka.

11. Kiransu da dadadan sunaye masu dadin gaske.

12. Ka zama kana biyawa matarka bukatarta ta kwanciyar jima'i, hakan zai kara muku nutsuwa da soyayya a zamantakewarku.

13. Ka yawaita addu'a ga matarka da zaman takewarku.

14. Ga kasance mai tunatar da matarka Allah, da kokarin bin tsarin addini domin gobenku ta yi kyau.


A karshe ku taya ni da addu'a, Allah ya bawa matata lafiya, ya sauketa lafiya dama sauran matan musulmi baki daya.


Iro Manu Rimi


Source /credit / sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Ina maza? To ga hanyar da zaka zama cikakken na miji nagari a wajan matar ka "

Post a Comment