ICPC na binciken ayyukan mazaɓa na N355 a Sakkwato

 Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, a jiya Talata ta fara bin diddigin ayyukan mazaɓu 10 da a ka bayar na sama da Naira miliyan 355 a jihar Sakkwato.


Ana gudanar da bincike kan matsayin ayyukan ne a karkashin mataki na 5 na aikin bibiya na ayyukan mazaɓu da ICPC ke yi a halin yanzu a jihohi 21.


Shugaban tawagar, Sa’idu Yahaya, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Sakkwato cewa za su duba ayyuka 10 a gundumomin Sanata guda biyu da mazabun tarayya biyar.


“An bayar da ayyukan ne a kan kudi N355, 391,657.95 kuma ana sa ran za a aiwatar da su gaba daya.


“Saboda haka, kungiyar da ta kunshi mambobi daga ICPC, Nigeria Institute of Quantity Surveyor, Civil Society Organisation, Media and Excutive Agency an umurce su da su bi diddigin ayyukan.


“Wannan shi ne domin a sa ido, bin diddigin ayyukan da kuma kimanta aikin da aka yi.


"Kazalika tantance adadin kwangilar da ƴan kwangila, gano kudaden da aka biya, gano matsayi da mutanen da ke cikin ayyukan," in ji Mista Yahaya.SOURCE :  DAILY NIGERIAN HAUSA FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments