Gwamnan Ebonyi ya bada garabasar N15,000 ga kowane ma'aikacin jihar
Gwamnan jihar Ebonyi, Cif David Umahi ya umurci a biya dukkanin ma’aikatan jihar albashin watan Nuwamba da Disamba tare kafin ranar 10 ga watan Disamba, 2022.


Gwamnan ya ce ya yi hakan ne albarkacin bikin kirsimeti da Kiristoci za su gudanar a cikin watan Disamba, ya kuma bayar da umurnin a kara wa dukkanin ma’aikatan jihar Naira 15,000 a matsayin garabasa.


Umurnin na a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Chooks Oko. Gwamnan ya ce ofishin babban akanta janar na jihar, Emeka Nwankwo, shi ne aka umurta da ya tabbatar da an biya kudi.

Source : DCL HAUSA ON FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments