Farashin kayan abinci ya fadi warwas a wasu kasuwannin Nijeriya

 

Farashin kayan abinci ya fadi warwas a wasu kasuwannin Nijeriya 


A Nijeriya farashin kayan abinci ya fadi warwas a wasu kasuwanin kasar kamar yadda majiyar DCL Hausa ta jaridar Daily trust ta ruwaito.


A makon jiya a kasuwar Dawanau ta jihar Kano an sayar da buhun masara kan Naira 26,000 yayin da yanzu ake sayar da shi a kan N21,000, buhun gero da aka sayar N27,000 yanzu ya dawo N23,000, farashin buhun waken ya sauka daga N37,000 zuwa N31,000.


Tun bayan yunkurin Gwamnatin Nijeriya na canja fasalin wasu daga cikin takardun kudi na Naira wasu attajiri suka bazama kasuwannin suke saye kayan abinci domin shigar da kudaden da ke hannunsu.

SOURCE : DUTSEN KURA COMMUNICATIONS LTD ON FACEBOOK.. 

0/Post a Comment/Comments