FALALAR ISTIGIFARI GA DAN ADAM

 FALALAR ISTIGIFARI

Na karanta cikin wata Qissa daga qissoshi i da wasu mutane su ka je wajen Ma'aiki ( Tsira da aminci maras iyaka ) su qara tabbata a gare shi daya-bayan-daya . Na farko yazo da maganar (fari) rashin ruwan-sama a karkararsu Shugaba (S.A.W) Ya umarce shi da yaje ya cewa mutanen garin su yi ta yawaita neman gafarar Ubangiji ( Istigifari) , na biyu ma yazo amma shi rashin samun zuri'a ne damuwarsa nan ma Shugaba (S.A.W) Ya sake umartarsa da abinda ya umarci na farkon . Anan zaune sai Sahabbai suka sake ganin wani Yazo a jigace yana cewa Shugaba talauci ya yi masa ka-ka-gida ko da na abinci ma bashi da shi balle na suttura , Nan ma Shugaban halittun Allah Ya sake cewa wan nan Bawan Allah ya je ya riqi istigifari .

Nan fa Sahabbai suka ce Ya Masoyin Allah " Mun ga mutane daban-daban har uku kowa yazo da matsala kace mu su su je suyi istigifari alhali matsalarsu daban-daban " Sai Ma'aikin Allah Yace :

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ‏( ﻓَﻘُﻠْﺖُ ﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻭﺍ ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻏَﻔَّﺎﺭًﺍ . ﻳُﺮْﺳِﻞِ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﻣِﺪْﺭَﺍﺭًﺍ . ﻭَﻳُﻤْﺪِﺩْﻛُﻢْ ﺑِﺄَﻣْﻮَﺍﻝٍ ﻭَﺑَﻨِﻴﻦَ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٍ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻟَﻜُﻢْ ﺃَﻧْﻬَﺎﺭًﺍ )

"Shi na ce, ´Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gafara ne."

"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga." "Kuma ya yalwata muku game da dukiya da diya,Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna."

Kun ga istigifari shine mai kauda duk wata matsala ya kuma jawo duk wani alkhairi don kada mu yi sake da yawaita shi....


Source :Auwal Abubakar fata nagari garko on Facebook. 


0/Post a Comment/Comments