Doguwa ya baiwa Garo da sauran waɗanda ya ɓata wa hakuri
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya baiwa mataimakin ɗan takarar gwamna na APC a jihar Kano, Murtala Sule Garo hakuri bisa jifan shi da kofin shayi yayin taron APC.


Haka ma DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa washegari ma sai da Doguwa ya doki Kakakin APC na jiha, Ahmad Aruwa a wani taro da ya hada a gidansa.


Sannan wani dan jarida, Abdullahi Yakubu, ya kai Doguwa kotu bisa ci masa zarafi a yayin taron manema labarai.


Sai dai kuma da ƴan sanda su ka kira Doguwa, ya je ya kuma baiwa dan jaridar hakuri, inda shi ma dan jaridar ya ce ya hakura.


Sannan, a yayin zaman sulhu tsakanin Daguwa da Garo a Abuja, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi musu fada ya kuma nemi kowa ya yafe wa kowa domin samun zaman lafiya a jam'iyar APC a Kano.


A zaman sulhun, Doguwa ya zargi Garo da ce masa ɗan mahauta, inda shi kuma Garo ya zargi Doguwa da zagin iyayensa.


Da ake sansancin, Doguwa ya zargin aikin asiri a matsayin dalilin da ya ke yin irin rigingimun, kamar yadda wata ma'ajiyar sirri ta shaida wa DAILY NIGERIAN.


Majiyar ta ce daga bisani dai aka sasanta su, inda shi kuma Garo ya nemi da Doguwa ya shiga gidan rediyo ya bashi hakuri domin kada mutane su ha kamar bai dauki iyayensa da muhimmanci ba.


Daga bisani Doguwa ya baiwa Garo hakuri ta kafafen yaɗa labarai.


Source : daily nigerian Hausa Facebook. 

0/Post a Comment/Comments