DAN AMUTUN TINIBU YA HANA HAYAR MOTOCIN SA DOMIN AYI JIGILAR YAN PDP ZUWA WAJAN KAMPE

 

Yadda Wani Dan A Mutun Tinubu Ya Ki Ba Da Hayar Motocinsa Domin A Yi Jigilar Magoya Bayan PDP Zuwa Wurin Tarbar Atiku Abubakar A BauchiA yayin wata ziyara da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai jihar Bauchi wani dan a mutun Bola Tinubu daga karamar hukumar Darazo, mai suna Muhammadu ya ki yadda ya bada motocin sa haya domin a kwashi magoya bayan PDP dake yankin nasa zuwa wurin tarbar Atiku duk da cewa biyansa za a yi.


Muhammadu ya kasance magoyin bayan Tinubu domin har ofis din yakin neman zaben sa ya bude a garin na Darazo.


Source :RARIYA ON FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments