--
DAGA YANZU, KUNGIYAR YAN TA'ADDA TA ISWAP TA DAINA KARBAR NAIRA SAI DAI SAIFA KUDIN NIJAR

DAGA YANZU, KUNGIYAR YAN TA'ADDA TA ISWAP TA DAINA KARBAR NAIRA SAI DAI SAIFA KUDIN NIJAR

>

 


Kungiyar Yan taadda ta ISWAP ta biyowa gwamnatin tarayya ta bayan gida inda ta haramtawa kanta cigaba da karbar kudin Naira daga wajen manoma da wadanda akayi garkuwa dasu.


Yanzu Yan ISWAP sun sanar da daukar matakin komawa karbar Kudin CEFA na Nijar maimakon Naira da za'a sauyawa Fasali a Najeriya.


Wani bincike ya nuna cewa Yan ta'addar na ISWAP da sauran Yan bindiga zaiyi wuya su iya kashe Tarin kudaden Naira da suka ajiye kafin wa'adin da gwamnatin tarayya ta gindaya na kwanaki 47 Dan dakatar da cigaba da karbar tsofaffin kudin naira da za'a sauyawa Fasali.


Me kuke ganin ya kamata gwamnatin tarayya yanzu Kuma tayi ,tunda kokarin Karya lagon yan ta'adda musamman tattalin arzikinsu na daya daga cikin abinda yasa gwamnatin ta bijiro da tsarin sauyawa naira Fasali?


Ko kuwa anyi kitso da kwarkwata ?


Source : Rahma Tv Facebook. 

0 Response to "DAGA YANZU, KUNGIYAR YAN TA'ADDA TA ISWAP TA DAINA KARBAR NAIRA SAI DAI SAIFA KUDIN NIJAR "

Post a Comment