DA ƊUMI-ƊUMINSA: Masu Canjin Kuɗin A Jihar Adamawa Sun Fara Ƙin Karɓar Kuɗaɗen Ƙasar Waje

 

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Masu Canjin Kuɗin A Jihar Adamawa Sun Fara Ƙin Karɓar Kuɗaɗen Ƙasar Waje


Masu canjin kuɗi a jihar Adamawa na ƙin amincewa da kuɗaɗen ƙasashen waje daga kwastomomi saboda rashin tabbas da ake samu a kasuwar kama-da-wane.


Wasu daga cikin ƴan canjin kuɗi da aka zanta da su a Kasuwar Zamani ta Jimeta da ke Yola, sun ce sun shiga cikin fargaba kwatsam da kuma ci gaba da faduwar dala, lamarin da ya janyo taɓarɓarewar kasuwan.


Shugaban ƙungiyar dillalan canji a jihar Adamawa, Lawan Mai Yasin, ya ce ƴan kasuwar sun tafka asara sosai bayan da suka sayi dala kan Naira 870 daga hannun ‘ƴan kasuwa kafin nan take ta faɗi zuwa N680.


Source : NIGER STATE MEDIA NEWS 24 FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments