APC ta kai ƙarar gidajen talabijin na Arise News da Channels TV bisa yaɗa wani shiri a kan Tinubu

 

APC ta kai ƙarar gidajen talabijin na Arise News da Channels TV bisa yaɗa wani shiri a kan Tinubu


Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, PCC, ta kai wa karar hukumar kula da yada labarai ta kasa, NBC, inda ya bukaci a hukunta gidajen talabijin na Arise News da Channels TV.


Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai da na kwamitin ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a yau Litinin a Abuja.


Ya ce kwamitin na neman NBC da ta saka wa gidajen Talabijin biyu takunkumi kan rahotannin karya da suka yi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, Bola Tinubu.


Takardar ta samu sa hannun mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa da hulda da jama’a na PCC, Dele Alake, inda ya aikewa darakta Janar Balarabe Ilelah.


Onanuga ya ce ana zargin gidajen talabijin din biyu da keta ka'idojin watsa labarai tare da ayyukansu.


Sanarwar ta faɗi ta bakin Alake na cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa Tinubu kamar yadda aka ruwaito kuma aka tattauna a gidajen Talabijin an riga an wanke shi a wata wasika da aka aika tsakanin Sufeto Janar na lokacin, Marigayi Tafa Balogun da gwamnatin Amurka.


Ya kara da cewa ci gaba da yada batun da babu shi saboda haka ya saba wa ka'idar watsa labarai ta NBC.

Source : daily nigerian Hausa on Facebook. 

0/Post a Comment/Comments