--
Anaci gaba da ce ce kuce akan kama wanda yai wa aisha buhari kazafi

Anaci gaba da ce ce kuce akan kama wanda yai wa aisha buhari kazafi

>

 

A Najeriya ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi a game da kama dalibin jami’ar tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu Muhammad wanda hukumomi suka yi a kan rubutun da ya yi a shafinsa na Twitter, inda ya zargi uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da cin kudin talakawa, tare ma da magana kan surarta.


Wasu dai na ganin matasa na wuce makadi da rawa, la'akari da yadda suke taba mutuncin shugabanni a shafukan sada zumunta, yayin da wasu kuma ke cewa ‘yanci ne na fadar albarkacin baki.


Yaya ku kuke kallon wannan lamari?


Source /credit /DW Hausa on Facebook. 

0 Response to "Anaci gaba da ce ce kuce akan kama wanda yai wa aisha buhari kazafi "

Post a Comment