--
 Abubuwan da Qatar ta tanadarwa Musulunci a wannan WorldCup ɗin ...

Abubuwan da Qatar ta tanadarwa Musulunci a wannan WorldCup ɗin ...

>

 
Abubuwan da Qatar ta tanadarwa Musulunci a wannan WorldCup ɗin ...


Daga Abubakar Saleh


1. A duk biranen da za'a buga wasan, Qatar ta rubuta Hadisan Annabi (SAW) a alluna ta yadda idan kazo wucewa sai ka karanta. 


2. Qatar ta hana shan ko siyar da giya a duk stadiums ɗin da za'a yi wasan.


3. A bango na ɗakunan hotels ma duk an rurrubuta hadisai da koyarwar musulunci 


4. An ɗauki ladanai masu zaƙin murya, sannan an kawo speakers har stadium saboda idan lokacin Sallah yayi za aji kiran sallah mai daɗi har a stadium.


5. Qatar ta tanadi wasu mutane/malamai kimanin 2000 waɗanda zasuyi da'awa na musuluntar da mutane, an tanada musu mobile cars da tanti tanti guda 20 na kai mutane masallaci da koya musu sallah da sauransu.


6. Qatar ta tanadi wajajen sallah da alwala a daf da dukkannin stadiums ɗin da za'ayi wasan domin masu kallo su samu saukin gabatar da sallah akan lokaci.

0 Response to " Abubuwan da Qatar ta tanadarwa Musulunci a wannan WorldCup ɗin ..."

Post a Comment